A Najeriya ana cece-kuce bisa dokar kayyade | Zamantakewa | DW | 25.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

A Najeriya ana cece-kuce bisa dokar kayyade

Yunkurin hallata tsarin iyali a kasar a matsayin hanyar rage yawan jama’a ta haifara da rarrabuwar kawuna tsakanin 'yan majalisar dokokin kasar

To ‘yan majlisar wakilan Najeriyar dai sun tafka muhawara mai zafi ne a kan matakin, bayan da dan majalisa Babatunde Gabriel Kolawole ya yi kokarin jawo hankali ga gwamnati, game da ci gaba da karuwar jama’ar kasar. Inda yace samar da doka a kan amfani da tsarin iyali zai iya taimakawa don shawo kan lamarin. Ya dai dage kan cewa a yadda Najeriyar ke samun hayayyafar jama’a, hasashe ya nuna cewa nan da shekara ta 2050, yawan al’ummar Najeriyar za su kai miliyan 433, abinda zai maida kasar matsayi na uku a yawan jama’a a duniya. To ko me ya sa mafi yawan ‘yan majalisar ke adawa da wannan yunkuri da ya sanya sanyata a gefe? Hon Sidi Yakubu Karasuwa, wakili ne daga jihar Yobe. Wanda yace ai shi a ganisa yawan jama'a shi ne karfin kasa, don haka bai goyi bayan dokar kayyade iyali ba.


Sanin cewa batun tsara iyali ko kuwa kayadde shi, lamari ne da ke da sarkakiyar gaske a Najeriya, musamman saboda dalilai na addini da ma al’adu irin na kasar da suke da kamanni da na wasu kasashen Afrika. Ko menene matsayin mabiyya addinin musulunci a kan wannan? Sheikh Tajudeen Muhammad Adigun shi ne shugaban cibiyar nazarin addinin Islama ta Fuad, kuma limamin masallacin da ke Anguwar Wuse a Abuja. Wanda yace a musulunci babu kayyade iyali, kuma yara arziki ne a garesu. To sai dai Sheikh Tajudeen ya ce akwai yanayin da ke sa a hallatawa musulmi amfani da tsarin don kare lafiya.


Su kansu mabiya addinin Krista batun kayadde iyali ya kasance wanda ke daukan hankali a tsakaninsu, abinda ya sanya kalonsa ta hanyoyi mabambanta. Rev Musa Asake shi ne sakatare janar na kungiyar Kristoci ta Najeriya wato CAN, ya bayyana matsayinsu a kan wannan batun, inda yace bisa dokar addinin Kirista kayyade iyali ba laifi bane, ya danganta ga ma'auratan idan suka dai-daita yadda suke so. To sai dai shi ma ya yi watsi batun kafa doka don kayyade iyali.


Da alamun wannan batu da ke cike da sarkakiyar gaske zai ci gaba da daukan hankalin al’ummar Najeriyar, a binda zai sanya gwamnati yin taka tsan-tsan da batun, saboda sanin cewa ba dadewa ba aka samu shawo kan wasu jihohin Najeriya suka amince da allurer rigakafin shan inna. Tuni da dadewa dai wannan batu na tsara iyali ke zama wanda ke daukan hankali a tsakanin mabiya addinin kasar.