A Najeriya an yanke hukuncin ɗaurin rai da rai kan wani dan kungiyar MEND
January 25, 2013A Najeriya kotun Tarayyar ƙasar ta yanke hukunci kan ɗaya daga cikin mutanen da aka zarga da kai harin ranar ɗaya ga watan oktoban shekara ta 2010. Mutumin mai suna Edmund Ebiware jami'an leƙen asirin ƙasar ne suka kamashi a Otel din Belingua kwana biyu bayan kai harin, wanda aka yi a dai-dai lokacin da ake gudanar bikin samun 'yancin kan Najeriya.
Maishari'a Gabriel Kolawole a shari'ar da ta dauki sa'o'i ukku, ya zargi Ebiware da laifin ƙin faɗawa hukumomin da suka dace a ƙasar, duk da cewa yana sane da za a kaiwa ƙasar harin ta'addanci. Don haka alƙalin ya yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai.
Wannan hukuncin dai bai yi wa wanda aka yankewa hukuncin daɗiba, inda ya yi ta kururwa abinda yasa jami'an tsaro suka amfani da ƙarfi don turashi cikin mota, kana aka yi awon gaba da shi izuwa gidan kaso.
Hukuncin yazo yan kwanaki bayan yankewa shugaban ƙungiyar yan yankin Naija Delta ta MEND Herry Okah makamancin wannan hukuncin a ƙasar Afirka Ta Kudu.
Mawallafi : Usman Shehu Usman
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe