A na ci gaba da fada a Ukraine | Labarai | DW | 17.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

A na ci gaba da fada a Ukraine

Akalla dakarun sojan gwamnatin Ukraine biyar ne aka kashe yayin da aka raunata wasu guda tara cikin sa'oi 24 a yankin da ake gwabza fada.

A yau Talata ne ake shiga rana ta karshe cikin wa'adin da aka ba wa dakarun sojan gwamnatin kasar Ukraine da mayakan sakai dan su fara janye tankokin yakinsu da suka girke a filin daga a gabashin kasar ta Ukraine, sai dai a cewar masu aiko da rahotanni ga kamfanin dillancin labarai na Associated Press ba bu alamun yin hakan ya zuwa yanzu.

Mai magana da yawun dakarun sojan kasar ta Ukraine Andriy Lysenko ya ce mayakan sakan masu samun goyon bayan kasar Rasha na ci gaba da kai farmaki ga dakarun sojan gwamnati a inda suka ja daga a kusa da garin Debaltsev. Ya kara da cewa akalla dakarun sojan na gwamnati biyar ne aka kashe yayin da aka raunata wasu guda tara cikin sa'oi 24 a yankin da ake gwabza fada.

A cewar Lysenko janye kayan yaki zai yiwune idan aka tsagaita bude wuta.