A Masar ana kara kuntatawa ′yan fafitika | Labarai | DW | 22.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

A Masar ana kara kuntatawa 'yan fafitika

Hukumomi a kasar Masar sun hana fita daga kasar akan wata yar fafitaka da ke cikin wadanda suka jagoranci boren kifar da gwamnatin Husni Mubarak

Asma Mahfouz wanda ke kan gaba cikin wadanda suka jagorancin juyin-juya halin shakara ta 2011, wanda ya kai ga kifar da gwamnatin Husni Mubarak, jami'an shige da ficen kasar suka hana mata izinin fita, bayan ta isa filin jiragen saman birnin Alkahira, da nufin yin bulaguro zuwa kasar Thailand. A cewar wani jami'in shige da fice, sunan Asma Mahfouz na cikin jerin wadanda gwamnatin sojoji suka bada izinin a hana musu fita daga Masar. Tun bayan kifar da gwamnatin Mohammad Mursi, sojojin da suka kwace iko suke cin zarafin duk wanda ya taka rawa a lokacin da aka yi boren karaw da gwamnatin kama karya. Akalla tun bayan kifar da gwamnatin ta Mursi, an hallaka mutane sama da 1400, yayinda aka tsare sama da mutane 15000.

AFP