A kasar Libiya sace jami′an gwamnati na karuwa | Labarai | DW | 03.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

A kasar Libiya sace jami'an gwamnati na karuwa

An sace wani babban alkali a kasar Libiya, inda harkokin tsaro ke karuwa

Libyan volunteers gesture as they raise a pre Gadhafi flag on the outskirts of the eastern town of Ras Lanouf, Libya, Tuesday, March 8, 2011. Forces loyal to Moammar Gadhafi have scored a significant victory, recapturing the closest city to the capital to have fallen in rebel hands. On another front near the opposition-held east, loyalists trying to stop anti-government fighters from advancing toward the capital pounded the rebels with airstrikes and rockets. (Foto:Tara Todras-Whitehill/AP/dapd)

Masu dauke da bindiga a Libiya

A kasar Libiya an sace shugaban kotun aikata manyan laifuka dake Benghazi birni na biyu mafi girma a kasar. Hukumomi suka ce an sace Abdulsalami Al-Mahdawi, bayan da wadanda suka sace shi suka nunamar bindiga, ko ya ransa ko ya bada kai. Jami'in da ya bada labarin wanda ya nemi a boye sunansa, yace yanzu lamarin ya fara gigitasu, domin kuwa a birnin ne aka sace shugaban yan sanda na lardin. Inda yace ya yi imanin cewa masu kaifin kishin Islama ne suka sace mutanen. Wani abokin alkalin da aka sace. yace alkalin yana da makiya da yawa, domin yana rike da takardun bincike na jami'an gwamnatin Gaddafi da aka kifar, kana alkalin yana binciken wasu masu kaifin kishin Islama da sauran wadanda ake zargi da aikata laifuka. Ministan cikin gidan Libiya Ashur Shway ya yi allah wadai da lamarin inda ya yi alkawarin kamo masu hannu a sace alkalin. Tun bayan kifar da gwamnatin Gandafi a bariya, batun tsaro ya lalace a Libiya inda ake kai hari kan yan sanda sojoji.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Saleh Umar Saleh