A karon farko wani madugun yaki ya mika kanshi | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 27.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

A karon farko wani madugun yaki ya mika kanshi

A ranar Litinin Bosco Ntaganda daga jamhuriyar demokradiyyar Kongo ya shiga harabar ofishin jakadancin Amirka dake birnin Kigali inda ya nema da a mika shi ga kotun duniya.

To bari mu fara da jaridar Die Tageszeitung wadda a babban labarinta ta mayar da hankali a kan kasar Kongo:

"A karon farko wani da kotun hukunta laifukan yakia duniya ke nema ruwa a jallo ya mika kansa da kansa. A ranar Litinin Bosco Ntaganda daga jamhuriyar demokradiyyar Kongo ya shiga harabar ofishin jakadancin Amirka dake Kigali babban birnin kasar Ruwanda inda ya nema da a mika shi ga kotun duniya ta binin The Hague. Ntaganda na zama wani madugun yaki na karshe da ya fice daga fagen yake yaken da ake fama da su a Kongo daga 1998 zuwa 2003. A bayan nan dai dan kabilar Tutsi daga yankin tuddan Masisi dake gabacin Kongo ya kasance kusa cikin kungyar 'yan tawayen M23, sai dai dukkan 'ya'yan kungiyar suna neman kai da shi. Tun a shekarar 2006 kotun duniya ta bayar da sammacin farko na kame Ntaganda bisa zargin daukar kananan yara aikin soja, sannan a shekarar 2012 aka ba da umarnin kama shi dangane da hannu kisan gillan da kungiyar UPC ta yi a shekarun 2002 da kuma 2003."

Baraka tsakanin 'ya'yan jam'iyar ANC

Jacob Zuma ya karfafa ikonsa inji jaridar Neue Zürcher Zeitung tana mai nuni da matakan da shugaban na Afirka ta Kudu ya dauka na nesanta kansa daga bangaren matasa na jam'iyar ANC.

South African President Jacob Zuma delivers a speech on November 15, 2012, in the Parliament in Cape Town. Zuma hit back at accusations he is failing the country before a raucous parliamentary hearing today, hours after allies torpedoed attempts to censure him. Facing accusations he mismanaged the economy, was AWOL during deadly labour unrest and wasted millions of taxpayers' money on upgrading a private residence, a visibly angered Zuma struck back. It was a rare flash of steel for the normally jovial leader. In one month Zuma faces the ANC's electoral conference, which will go a long way toward deciding whether he remains president of Africa's largest economy for another five years. AFP PHOTO / STRINGER (Photo credit should read STRINGER/AFP/Getty Images)

Jacob Zuma na neman yin tazarce a shekarar 2014

"Shugaban Afirka ta Kudu na ci-gaba da aiki sake fasalta tsare-tsaren jam'iyar ANC dake mulki domin a sake zabensa a farkon shekara ta 2014. Watanni uku baan babban taron jam'iyar a Mangaung inda masu sukar lamirin Zuma suka kwashi kashinsu a hannu, a karshen mako jam'iyar ANC ta rusa kwamitin shugabannin kungiyar matasanta da kuma kusoshin jam'iyar a lardin Limpopo. Ko da ya ka a hukumance an dauki wannan mataki bisa dalilai na rashin da'a daga bangaren matasan, amma manazarta sun yi nuni da cewa matasan da ma wakilan jam'iyar daga Limpopo sun goyi bayan da a sauke Zuma a lokacin babban taron jam'iyar da ya gabata. Yanzu haka dai shugaban mai shekaru 70 ya dora mutanensa ne a kan manyan mukaman jam'iyar ta ANC."

Shugaba Gauck a birnin Addis Ababa

GettyImages 163886258 ADDIS ABABA, ETHIOPIA - MARCH 17: German President Joachim Gauck (L) talks with Ethiopian Prime Minister Hailemariam Desalegn before dinner at the Presidential Palace on the first day of his official visit on March 17, 2013 in Addis Ababa, Ethiopia. President Gauck and his partner, German First Lady Daniela Schadt, are in Ethiopia for a four-day state visit. (Photo by Sean Gallup/Getty Images)

Ganawar keke da keke tsakanin Gauck da Desalegn

Ita kuwa jaridar Berliner Zeitung tsokaci ta yi game da ziyarar kwanaki hudu da shugaban tarayyar Jamus Joachim Gauch ya kai kasar Habasha a wannan mako, inda ta fara da cewa shugaban Jamus ya yi takatsantsan wajen sukar tsarin demokradiyyar Habasha ba tare da fuskantar fushin masu mulki ba, sannan sai ta ci-gaba kamar haka.

"Tattaunawar da shugaban na Jamus Joachim Gauck yayi da Firaministan Habasha Hailemariam Desalegn, ta yi armashi inda ya tabo batutuwan da suka shafi karancin 'yanci ga 'yan adawa da sanya wa kungiyoyin kare hakkin bil Adama tarnaki da tursasawa 'yan jarida da mawallafa har izuwa kame wasu masu zanga-zanga a kwanakin baya bayan nan. Abin mamaki kuwa shi ne firaministan na Habasha ya saurari koke koken na shugaban Jamus, inda ya ce ba za a iya aron demokradiyya daga Jamus ko Italiya ba, dole ne ta fito daga cikin kasar, ya ce a halin yanzu abin da gwamnatinsa ta fi ba wa fifiko shi ne yaki da talauci."

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Halima Balaraba Abbas