A Kamaru mutane 70 sun mutu a hadarin jirgin kasa | Labarai | DW | 22.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

A Kamaru mutane 70 sun mutu a hadarin jirgin kasa

Ministan sufuri na kasar Edgar Alain Mebe Ngo'o ya tabbatar da rasuwar mutane 55 a hadarin jirgin kasa tsakanin Yaounde da Duala a ranar Juma'a.

Akalla mutane 55 suka mutu wasu 600 kuma suka sami raunuka a hadarin jirgin kasa a Kamaru a jiya Juma'a. Hadarin ya faru ne sakamakon gocewar da jirgin ya yi daga layin dogo. Jirgin wanda ke makare da mutane saboda tsaikon da aka samu a hanyoyin mota saboda karyewar wata gada, ya taso ne daga Yaounde babban birnin kasar zuwa Douala cibiyar kasuwanci a cewar ministan sufuri Edgar Alain Mebe Ngo'o.

Hukumomin agaji da jami'an tsaro sun taimaka wajen Kai dauki cikin gaggawa.

Jami'an jirgin kasan sun ce jirgin na dauke da fasinjoji 1, 300 maimakon 600 da ya kamata ya dauka.

Kawo yanzu dai ba'a tabbatar da musabbabin hadarin ba.

Ministan lafiya na kasar ta Kaaru Andre Mama Fouda yace gwamnati za ta dauki bada magani ga wadanda suka sami raunuka.