A kalla mutane 688 sun halaka a girgizar kasar Nepal | Labarai | DW | 25.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

A kalla mutane 688 sun halaka a girgizar kasar Nepal

Wannan bala'i dai ya zama mafi muni cikin shekaru tamanin a tarihin kasar da ke zama matalauciya daga yankin kudancin na Asiya.

Nepal Kathmandu Starkes Erdbeben Durbar Square

Al'umma cikin rudani bayan girgizar kasa

Wata mummunar girgizar kasa da ta afkawa kasar Nepal da ke a kudancin yankin Asiya a ranar Asabar dinnan, ta yi sanadin kisan akalla mutane 718 a bala'in da ya shafi kusan kasashen hudu makota da lalata gine-gine da hanyoyi, abin da kuma ya sanya zamowar kankara cikin gaggawa daga tsaunin Mount Everest .

Wannan bala'i dai ya zama mafi muni cikin shekaru tamanin a tarihin kasar da ke zama matalauciya daga yankin kudancin na Asiya.

A kalla mutane 688 daga kasar ta Nepal sun halaka kamar yadda 'yan sanda suka tababatar wasu 20 suma sun rasu a Indiya shida a yankin Tibet wasu guda biyu a Bangladesh, wasu 'yan kasar China biyu suma sun rasu akan iyakar Nepal da China.

'Yan mintuna ne dai kafin karfe shabiyun rana girgizar mai karfin maki 7.8 ta afku a yankin kwarin Kathamandu mai yawan jama'a.