A kai harin kunar bakin wake a Kamarun | Labarai | DW | 25.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

A kai harin kunar bakin wake a Kamarun

Wani harin kunar bakin wake da aka kai a kasuwar garin Bodo da ke yankin Arewa mai nisa, ya yi sanadiyyar rasuwar mutane a kalla 29 tare da jikkata wasu da dama.

Wani da ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Reuters lamarin, ya ce an samu akalla fashewar abubuwa sun kai guda uku zuwa hudu, kuma bai san adadin wadanda suka rasu ba. Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da garin na Bodo ke fuskantar wannan matsala ba, inda a karshen watan Disamba ma dai wani dan kunar bakin wake ya tashi bam din da ke jikinsa, sai dai ba a samu asarar rayuka ba.