A Hong Kong ana dakon tattaunawa | Labarai | DW | 21.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

A Hong Kong ana dakon tattaunawa

Bayan tsawon lokaci na zanga-zangar da ta durkusar da harkokin kasuwancin yankin Hong Kong, a yau Talata ana jiran ganin tattaunawa da za a yada ta kafar talibijin tsakanin gwamnati da masu fafutuka.

Masu fafutukar rajin kafa dimokradiya a Hong Kong sun tsaya a tituna ana kallon-kallo da jami'an 'yan sanda gabannin fara tattataunawa da bangaren gwamnati da shugabannin masu fafutukar a ranar Talatan nan.

Babu dai labarin gwabzawa tasakanin masu fafutukar da 'yan sanda a yankin kasuwancin na Mong Kok a mashigar teku ta Kowloon, daya daga cikin manyan wurare uku da wannan zanga-zanga tafi kamari.

A yammacin jiya Litinin ne babbar kotun ta Hong Kong ta bada umarni ga masu zanga-zangar da su kauracewa dandalin da suka kafa a yankin na Mong Kok.

Tattaunawar dai da aka tsara a yau Talata tsakanin masu rajin dimokradiya da bangaren gwamnati, za a yada ta ne kai tsaye ta kafar talabijin inda za a tattauna kan batun tsare-tsare na zaben kasar.