A gabar Italiya an ceto bakin haure 6000 | Labarai | DW | 04.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

A gabar Italiya an ceto bakin haure 6000

Kamar yadda kididdigar hukumar kasa da kasa kan 'yan gudun hijira ta nunar, zuwa karshen Satimbar da ya gabata bakin haure 132,000 ne su ka isa Italiya.

Mittelmeer Mehr als 6000 Bootsflüchtlinge gerettet (picture alliance/Pacific Press/A. Di Vincenzo)

Bakin haure kan dauki kasada da bin ta teku dan isa Turai ko ta halin kaka

Fiye da bakin haure 6000 ne aka sami damar ceto su bayan baro gabar teku a Libiya a ranar Litinin kamar yadda jami'an da ke lura da gabar teku a Italiya suka bayyana.

Mutanen 6,055 sun samu kansu bayan baro gabar teku a Libiya inda suka nausa teku da tazarar kimanin kilomita 88 daga Tripoli babban birnin kasar ta Libiya a cewar jawaban jami'an da ke lura da gabar teku.

Mutanen dai na tafe ne cikin wasu kwale-kwale da ake daukar kasada da su marasa inganci a shiga teku dan zuwa Turai. Aikin ceton dai ya kasace na hadin gwiwa tsakanin dakarun da ke lura da gabar tekun ta Italiya da dakarun hana fasakaurin jama'a ta teku daga Kungiyar EU da cibiyar da ke kare iyakokin na Turai da wasu kungiyoyi na agaji.