A cikin watan fabrairu za´a yi zaben gama gari na farko a Uganda | Labarai | DW | 17.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

A cikin watan fabrairu za´a yi zaben gama gari na farko a Uganda

Hukumar zaben Uganda ta ce a cikin watan fabrairun badi za´a gudanar da zaben jam´iyu da yawa na farko a cikin kasar. Wani babban jami´in hukumar zaben kasar ya fadawa kamfanin dillancin labarun AFP cewa a ranar 23 ga watan fabrairun shekara ta 2006 za´a gudanar da zabukan shugaba kasa da na´yan majalisar dokoki. A jiya juma´a aka fara yakin neman zaben wanda za´a kammala a ranar 21 ga watan fabrairu, domin ba da damar gudanar da zabukan gama gari na farko tun bayan da Uganda ta farfado da tsarin jam´iyu barkatai a wata kuri´ar raba gardama da ta gudanar a cikin watan yuli. Lokacin ya hanbarad da gwamnatin mulkin soji a shekarar 1986 shugaba Yoweri Museveni ya haramta ayyukan jam´iyun siyasa a cikin kasar.