1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A Burundi gwamnatin tazarce ta fara aiki

Gazali Abdou TasawaAugust 25, 2015

Kasa da mako daya bayan rantsar da shugaba Pierre Nkurunziza a sabon wa'adi mulki tuni ya kafa sabuwar gwamnatinsa wacce ke da mambobi 20.

https://p.dw.com/p/1GLOB
Burundi Vereidigung Präsident Nkurunziza
Hoto: Reuters/E. Ngendakumana

Sabuwar majalisar ministocin tana da mata 6 kana da maza 14 duk daga kabilun Tutsi da Hutu. Wannan kuwa wani mataki na kiyaye kundin tsarin mulkin kasar, inda ya tilasta saka mata da kuma raba madafan iko a tsakanin manyan kabilun kasar biyu.

Mutanen da gwamnatin farko a mulkin ta-zarcen na shugaba Nkurunziza, an ganin akasarinsu 'yan kanzagin shugaban ne da kuma masu tsatsauran ra'ayi adawa da Alain Guillaume Bunyoni tsohon soja kana tsohon daraktan farko na hukumar 'yan sandar kasar ta Burundi, bayan fitowar kasar daga yakin basasa da ya samu mukamin ministan tsaro na kasa.

Sai dai tun ba a je ko ina ba, kawancan jam'iyyun adawar na baggaren tsohon madugun 'yan adawar kasar wanda daga baya ya bada kai bori ya hau ta hanyar halartar zabe dama karbar mukamin mataimakin sabuwar majalisar dokokin kasar ya tashi da kujeru biyar daga cikin 20 da majalissar ministocin kasar. Amma fa 'yan adawan kasar sun soma bayyana sabuwar gwamnatin kasar da kasan cewa haramtacciya, a cewarsu nadin ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar, wanda ya tanadi sai wakillan jam'iyyun da doka ta amince da su ne ke iya hawa mukamin minista a kasar. Sabanin hakan alhali a yanzu wasu ministocin da aka nada, an basu mukaman ne da sunan kawancen jam'iyyunsu. Leon Nguendakumana na daya daga cikin shugabannin 'yan adawar kasar ta Burundi.

"Ya ce ba a kiyaye kundin tsarin milkin kasarmu ba, kuma wannan abu ne da ba za mu taba amincewa da shi ba. Mu a bangarenmu wannan gwamnati haramtacciya ce, dan haka za mu ci gaba da gwagwarmayar siyasarmu. Ta yadda muka kori Buyoya daga mulki, shi ma wannan ta haka za mu kore shi."

Tuni dai bangaren gwamnatin kasar ta Burundi ya yi watsi da zargin keta haddin kundin tsarin mulki, a cikin matakin nada sabuwar gwamnatin kasar. Willy Nyamitwe ya kare matakin gwamnatin yana mai cewa.

"Ya ce wannan gwamnatin ta halal ce a kundin tsarin mulki, domin tun kafin a kafa ta sai da shugaban kasa ya bukaci kotun tsarin mulki ya fassara anniyar da shugaban kasa ke son yi"

Burundi Oppositionsführer Agathon Rwasa
Agathon Rwasa, madugun 'yan adawan BurundiHoto: Getty Images/AFP/C.de Souza

A wani abu da ke nuna sauyi daga bangaren 'yan adawa, da dama daga cikin masu adawa da ta-zarcen shugaba Pierre Nkurunziza sun bada shawarar ci gaba da kalubalantarsa, ba tare da gudanar da irin tarzomar da aka gani a baya ba.