30 ga Mayu ne za a yanke wa Habre hukunci | Labarai | DW | 12.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

30 ga Mayu ne za a yanke wa Habre hukunci

Lawyoyin tsohon shugaban Chadi Hissene Habre sun nemi a wankeshi daga zargin da ake yi masa, yayin da mai shigar da kara ya nemi kotu ta yi masa daurin rai da rai.

A ranar Alhamis ce dai kotun ta musamman ta Afirka da ke Dakar babban birnin kasar Senegal ta kammala wannan shari'a inda kuma za ta bayar da sakamakon a nan gaba. A ranar Laraba dai da ta gabata, babban Alkali na musamman Mbacké Fall, ya nemi da a yanke wa tsohon shugaban kasar hukuncin daurin rai da rai, abin da ya kira hukunci daidai da laifukan da ya aikata lokacin mulkinsa daga shekara ta 1982 zuwa 1990.

Wannan dai shi ne karo na farko a duniya da aka yi shari'ar wani tsofon shugaban kasa a gaban kotun wata kasa, bisa laifin da ya yi wa al'ummar kasarsa. A cewar shugaban kotun dan kasar Burkina Faso Gberdao Gustave Kam, za su bayar da sakamakon ne a ranar 30 ga watan Mayu mai zuwa.