2015: An hallaka ′yan jarida 110 yayin da suke aiki | Siyasa | DW | 29.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

2015: An hallaka 'yan jarida 110 yayin da suke aiki

Kungiyar kare hakkin 'yan jaridar nan ta Reporteurs Sans Frontiere (RSF) ta ce kimanin 'yan jarida 110 suka rasu a bakin aiki a shekarar nan da muke shirin bankwana da ita.

Kungiyar ta RSF ta bayyana wadannan alkalumma ne a cikin rahotonta na shekara-shekara da ta wallafa a wannan Talata (29.12.15) inda ta bayyana cewar kasar Iraki ce ke kan gaba wajen yawan manema labarai da suka gamu da ajlinsu a bakin aiki. Yawan 'yan jaridar na Iraki da suka rasu dai sun kai goma sha daya inji rahoton na RSF.

Siriya wadda ke fama da yakin basasa da ya shiga shekararsa ta hudu ita ce ta da yawan 'yan jarida goma yayin da Faransa ke biye mata unda 'yan jaridar takwas suka rasu a sassa daban-daban na kasar yayi da suke aikinsu na farautar labarai a ita wannan shekara ta 2015.

Wadannan alkalumman da kungiyar ta Reporteurs Sans Frontiere (RSF) na shekara ta 2015 sun sha gaban na shekara ta 2014 da ta gabata kungiyar ta ce an hallaka inda aka hallaka 'yan jarida 66. Wannan yanayi na mace-macen da ake samu ta 'yan jarida a bakin aikinsu dai abu ne da ke da tada hankali inji kungiyar, hakan ne ma ya sanya ta ce akwai bukatar ganin Majalsiar Dinkin Duniya ta nada wakilin musamman na kare 'yancin 'yan jarida.Manema labarai ma dai da ke sassa daban na duniya ciki kuwa har da kasashen da ke nahiyar Afirka sun bukaci da a a duba yanayin da 'yan jarida ke aiki don inganta shi wanda a cewarsu hakan zai taimaka wajen kaucewa cin zarafin da suke fuskanta sannan kuma a dauki matakai na ganin an kaucewa hallaka su yayin da suke gudanar da aiki ko da kuwa a wuraren da ake fama da tashin hankali ne.