Ɓullar zazzabi makamancin Ebola Uganda | Labarai | DW | 05.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ɓullar zazzabi makamancin Ebola Uganda

Wani zazzaɓi makamacin na Ebola da ake yi wa laƙkabi da Marburg ya hallaka wani jami'in kiwon lafiya a birnin Kampala na ƙasar Uganda.

Elektronenmikroskopische Aufnahme des Marburg-Virus

Kwayar cutar zazzabin Marburg da ke saurin kisa

Ma'aikatar kiwon lafiyar Ugandan da ta tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Reuters wannan labarin ta ce mutumin da shekaru talatin, ya rasu ne a ƙarshen watan jiya kuma tuni aka gano tare da killace mutane tamanin wanda galibinsu abokan aikinsa ne da ya yi hulda da su kafin ya rasu.

Masana kiwon lafiya a ƙasar dai sun ce zazzaɓin wanda ke da saurin kisa bai da magani kuma ya kan fara ne da alamu irin na Ebola wanda suka haɗa da zazzafan ciwon kai da zazzaɓi da amai da gudawa na jini kuma galibi ya kan bayyana ne makonni biyu bayan kamuwa da shi kuma a kan yaɗa shi ta hanyar ruwan da ke fita ta kafofin jikin mutum ko mu'amula da dabbobin irinsu biri da ke ɗauke kwayoyin cutar.