Ƙwato garin Gwoza daga Boko Haram | Labarai | DW | 27.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙwato garin Gwoza daga Boko Haram

Dakarun Najeriya sun sanar da ƙwato garin Gwoza daga hannun Ƙungiyar Boko Haram da ke gwagwarmaya da makamai a ƙasar.

Kakakin rundunar sojojin ƙasar Chris Olukolade ne ya tabbatar da hakan inda ya ce sun hallaka mayaƙan kungiyar ta Boko Haram masu yawa tare da kama wasu. Haka nan ma Olukolade ya ce sun ƙwace manyan makamai masu tarin yawa daga 'ya'yan kungiyar a yayin fafattawar da suka yi da su kana suna ci gaba da gudanar da gaggarumin bincike domin gano inda ragowar 'yan ta'addan da suka tsere suka ɓuya. Wannan nasara dai da sojojin Najeriyar suka yi ikirarin samu ta ƙwato garin na Gwoza na zuwa ne ƙasa da sa'oi 24 da fara kaɗa ƙuri'a a zaɓukan shugaban ƙasa da na 'yan majalisun dokoki a kasar, kana kwana biyu bayan da Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriyar ya tabbatar da cewa sojojin za su ƙwato garin na Gwoza a wannan Jumma'a, abin da ya sanya 'yan Najeriyar da dama yin watsi da batun cewar sojojin sun fafatta da 'yan Boko Haram ɗin domin ƙwato Gwozan. Wani farar hula da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa manema labarai cewar sunji labarin an ƙwato garin Gwoza sai dai har yanzu suna mamakin hakan, domin babu wata shaida da ke nuni da haka.