Ƙurdawa na riƙe da garin Kobane | Labarai | DW | 09.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙurdawa na riƙe da garin Kobane

Mayaƙan sun ci gaba da iko da birnin duk da farmakin da Ƙungiyar IS ta kai musu tare da yi musu ƙawanya.

Wani kakakin ma'aikatar tsaron Amrika ta Pentagone Amiral John Kirby ya yi gargaɗin cewar,hare-hare ta jiragen sama na yaƙi na Amirkan da ƙawayenta ba za su isa ba, wajen hana garin na Kobane faɗawa cikin hannu 'yan tawayen.

To sai dai a wani taron manema labarai da ya yi shugaba Barack Obama ya ce tafiya ce mai nisa.Sannan kuma ya ce za su ci gaba da kai hare-hare tare da ƙawayensu a kan masu jihadin har sai haƙarsu ta cimma ruwa.