Ƙungiyar ′yan tawayen M23 na Kwango na cikin halin tsaka mai wuya | Labarai | DW | 02.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙungiyar 'yan tawayen M23 na Kwango na cikin halin tsaka mai wuya

Dakarun gwamnati a Kwango sun ƙwace iko da garin Rutshuru da ke a yankin gabanshin ƙasar, arewa da Goma,ba tare da shan wani gumurzu ba.

Sojojin gwamnatin sun yi amfani da saɓanin da ke tsakanin dakarun ƙungiyar ta M23 domin karɓe iko da garin, wanda 'yan tawayen ke riƙe da shi tun a cikin watan Yulin da ya gabata.

Masu aiko da rahotannin sun ce mazauna garin sun yi tarbo mai daraja ga sojojin gwamnatin,waɗanda suka shiga birnin da 'yan tawayen da ke cikinsa suka tsere suka bar shi, saboda faɗan da ɓangarorin biyu suke kabsawa.Tsakanin magoya bayan janar Sultanin Makenka da Jean Marie Runiga masu yin rikici kan shugabancin ƙungiyar ta M23.tun lokacin da a ka rataɓa hannu a kan wata yarjejeniyar zaman lafiya a ƙasar Habasha tsakanin ƙasashen da ke maƙoftaka da Kwangon domin sake dawo da zaman lafiya a ƙasar.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammad Nasiru Awal