Ƙungiyar Tarayyar Afirka na tattaunawa | Siyasa | DW | 29.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ƙungiyar Tarayyar Afirka na tattaunawa

Taron shugabannin ƙasashen Afirka na shekara-shekara da ke gudana a ƙarshen mako a birnin Addis Ababa na ƙasar Habasha na duba rikice-rikicen da nahiyar Afirka ke fama da su.

Ko da yake wasu batutuwan an san su, amma taron kolin tarayyar Afirka AU karo na 26 zai ga sabbin abubuwa. Domin a karon farko cikin tarihin ƙungiyar wakilanta za su amince da girke wata rundunar zaman lafiya duk da adawar gwamnatin da abin ya shafa wato Burundi, kamar yadda sashe na huɗu na ƙuduri AU ya tanada. Za a buƙaci rinjayen kashi biyu bisa uku a ƙuri'ar da za a kaɗa don rundunar mai suna "African Prevention and Protection Mission in Burundi" wato MAPROBU a taƙaice ya fara aiki. Sai dai har yanzu ba a fayyace ƙasashen da za su ba da karo karon sojojinsu ga wannan rununa ba.

Ƙoƙarin ganin gwamnatin Burindi ta amince da a tura sojojin

A makon da ya gabata wata tawagar Kwamitin Sulhun MDD ta je Burundi inda ta nemi amincewar gwamnatin shugaba Pierre Nkurunziza dangane da girke rundunar mai dakaru 5000. Sai dai gwamnatin ƙasar na yi wa rundunar ta MAPROBU kallon dakarun maamye saboda haka ta yin watsi da aikinta. Smail Chergui shi ne kwamshinan harkokin tsaro da zaman lafiya na ƙungiyar AU.

"Dakarun shiga tsakani za su ƙoƙarin maido da zaman lafiya a ƙasar. Dole ne mu samar da hanyoyin cimma masalaha ta bai ɗaya, ta yadda za mu taɓo dukkan batutuwan da suka wajaba. Idan ba mu yi haka ƙasar na fuskantar barazanar rugujewa."

Taron zai kuma duba wasu rikice-rikicen da nahiyar ke fuskanta

A matakin farko ƙudurin AU dai ya tanadi girke jami'ai 100 da suka hada da soji da masu sa ido kan batun kare 'yancin dan Adam zuwa ƙasar ta Burundi musamman a kusa da kan iyakarta da ƙasar Ruwanda.Halleluyah Lulie da ke manazarcin harkokin tsaro a ƙasar Habasha na mai ra'ayin cewar sassan biyu za su cimma matsaya.

"Ina sa ran cewar gwamnatin Burundi da Ƙungiyar Tarayyar Afirka za su daidaita kan wasu batutuwa don su cimma yarjejeniyar da za ta kai ga aiwatar da matakan da majalisar tsaro da zaman lafiya ta AU ta dauka."

Muhimmi batu na biyu da taron kolin AU na wannan shekara da ke zama shekarar zabuka a Ƙasashen Afirka zai tabo shi ne rikicin Sudan ta Kudu da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa. Shugaba Salva Kiir ya yi gaban kanshi inda ya ƙara yawan jihohin ƙasar daga 10 zuwa 28, matakin da masanin harkokin tsaro na Habasha Halelleluyah Lulie ya ce ya mayar da hannu agogo baya a ƙoƙarin sasanta rikicin ƙasar.

Sauti da bidiyo akan labarin