Ƙungiyar OSCE ta hango wata barazana a rikicin Ukraine | Labarai | DW | 27.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙungiyar OSCE ta hango wata barazana a rikicin Ukraine

Ƙungiyar OSCE ta ƙasashen Turai ta yi gargaɗin kan yiyuwar ɓarkewar sabon faɗa a Ukraine

Manzon musamman na ƙungiyar nan ta tsaro da haɗin kan ƙasashen Turai wato OSCE da ke ƙasar Ukraine, ta yi gargaɗi kan yiwuwar ɓarkewar sabon faɗa a Ukraine, a dai dai lokacin da ake batu na tsagaita buɗa wuta a gabashin Ukraine ɗin.

Jami'ar diflomasiyar wato Heidi Tagliyavina, da ta shaidawa kwamitin tsaron Majalisar Ɗinkin Duniya cewa akwai alamun dakatar da faɗa a gabashin Ukraine ɗin tare ma da sakin fursunoni da janye manyan makamai, ta ce ta hango alamun taɓarɓarewa lamura a yankin, don a cewarta ko a yau Jumma'a ma sai da aka kashe sojojin Ukraine uku a wata fitina da ta kaure tsakaninsu da 'yan tawaye magoya bayan Rasha.