Ƙungiyar NATO na tuntuɓar girke dakarun Jamus a kudancin Afghanistan. | Labarai | DW | 16.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙungiyar NATO na tuntuɓar girke dakarun Jamus a kudancin Afghanistan.

A fafatawar da dakarun NATO ke ta yi da mayaƙan ƙungiyar Taliban a kudancin Afghanistan, inda kuma bisa dukkan alamu, mayaƙan Taliban ɗin ke ta ƙalubalantarsu, hukumar ƙungiyar na tuntuɓar ƙara yawan dakarun da ta girke a ƙasar. Rahotannin da muka samu daga birnmin Kabul na nuna cewa, manyan hafsoshin rundunar soji na kungiyar ta NATO na auna yiwuwar maido da wasu daga cikin dakarun Jamus da ke girke a arewacin ƙasar, inda aka fi kwanciyar hankali, zuwa yankunan kudancin ƙasar, inda a halin yanzu, kusan a ko yaushe sai mayaƙan Taliban ɗin sun kai wa rukunan NATOn hari. Tsohon ministan tsaron Jamus, Peter Struck ya yi fira da maneman labarai game da wannan shirin da ƙungiyar ƙawance ta NATOn ke muhawara a kansa:-

„Dakarun Jamus dai na da farin jini a arewacin Afghanistan, saboda ba faɗa kawai suke yi ko kuma nuna ƙarfin soji ba. Suna taimakawa wajen horad da jami’an ’yan sanda da na sojin ƙasar. Na sha tattauna dabarunmu da tsohon ministan tsaron Amirka Rumsfeld. Amma shi a ganinsa, aikin da muke yi ba na soji ba ne, na fararen hula ne. Ya fi gwammace wa fafatawa irin ta soji. Sabili da haka ne kuwa, muka gaza shawo kan matsalar Taliban. Halin sassaucin tsamari da kwanciyar hankalin da muke samu a arewacin Afghanistan inda dakarunmu ke girke dai, wato, yana sa ɓangarori da dama su yi ta sanya alamar tambaya kan manufar da Amirka ke bi a wasu yankuna daban na ƙasar.