Ƙungiyar MEND ta sake kame wasu jami´an haƙar man petur a Niger Delta | Labarai | DW | 03.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙungiyar MEND ta sake kame wasu jami´an haƙar man petur a Niger Delta

Matasan dake fafatakar ƙwato yancin yankin Niger Delta, sun ƙara yin garkuwa da wasu jami´an kampanonin man petur na ƙasshen ƙetare.

Sanarwar daga opishin ministan harakokin wajen Korea ta kudu, ta nunar da cewa, da asubahin yau matasan na ƙungiyar MEND sun yi awan gaba da yan ƙasar Korea ta kudu 3 da yan Philipines guda 8.

Kungiyar ta yi awan gaba da wannan mutane, bayan gumurzu tare da sojojin gwamnati kussa da Patakol..

Mutanen da aka kama yau, sun haɗa da Chung Tae-Young wani babban darakta Jannar na kampanin Daewoo na Korewa ta kudu, ayayin da ya ke cikin bullaguro a yankin na Niger Delta.

Rikicin Niger Delta, a shekara da ta gabata, ya yi sanadiyar asara kashi 1 bisa 3, na yawan man petur ɗin da ya kamata Nigeria ta sayar a kasuwanin dunia, wanda aka ƙiyasta kuɗin sa, kimanin dalla milion dubu 4, da rabi.