ƙungiyar Mend ta bayyana kashe sojoji 9 na gwamnatin Nigeria | Labarai | DW | 09.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

ƙungiyar Mend ta bayyana kashe sojoji 9 na gwamnatin Nigeria

A Tarayya Nigeria, matasa masu nema yancin yankin Niger Delta, sun bayyana kashe sojoji 9 na gwamnati, a sakamakon wata arangama da su ka yi.

Kakakin ƙungiyar Mend ya ce, sun hallaka wannan sojoji a cikin wata taho mu gama, ta tsawon mintina 45,da su ka yi, kussa da yankin Okerenkoko, bayan da a cewar sa, tawagar sojojin ta farma dakarun su.

Ya ce kuma wannan saban hari , ya kara harzuka aniyar su, ta ƙwatar yancin Niger Delta, mai arzikin man petur.

Idan dai ba a manta ba, har yanzu ƙungiyar Mend, na tsare da jami´ai 3, na ƙasashen ƙetare da su ka haɗa da ɗaya na Britania,da 2 Amurikawa.

A ɗaya wajen kuma, rahotani sun bayana cewa gwammnatin tarayya ta hidda Jannar Elias Zamani shugaban rundunar gwammnati a yankin Niger Delta, bayan an tuhume shi, da hannu cikin satar man petur.