Ƙungiyar ISIS ta ƙwaci iko da garin Al-Qaim | Labarai | DW | 21.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙungiyar ISIS ta ƙwaci iko da garin Al-Qaim

'Yan tawayen Sunni na Iraƙi, sun samu nasarar ƙwace wani ofishin bincike na Al-Qaïm, da ke kan iyaka da Siriya.

Yayin da aka shiga cikin kwanaki na 13 da mamayar yankunan ƙasar da ƙungiyar ta ke yi, faɗa na ƙara yin muni a ƙasar ta Iraƙi tsakanin dakarun gwamnatin da na 'yan tawayen.

A halin yanzu dai cibiyoyin bincike biyu ne kaɗai suka rage, a kan iyakar ƙasar Iraƙi da Siriya mai tsawon kilomita 600 wanda ɗaya ke hannun dakarun da ke yin biyayya ga gwamnatin ƙasar, da kuma ɗaya da ke hannun Kurdawa.'Yan tawayen na Sunni, sun karɓe birnin Falluja ga baki ɗaya da kuma wasu ƙarin yankuna da ke a kusa da birnin.

Mawallafi : Salissou Boukari
Edita : Abdourahamane Hassane