Ƙungiyar IS ta harbe matasa biyu a IraƘi | Labarai | DW | 21.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙungiyar IS ta harbe matasa biyu a IraƘi

A bainan jama'a ne masu kaifin kishin addini na IS suka harbe matasa biyu har lahira a lardin Kirkuk bisa zargin haɗa Kai da sojojin Iraki.

Mayakan Ƙungiyar IS da ke gagwarmaya da makamai sun bindige wasu matasa biyu har lahira a bainan jama'a, bisa zarginsu da suke yi da haɗa kai da abokan gabansu na Iraƙi wato jami'an tsaro. Shaidun suka ce a dandalin wata sananniyar kasuwa ta Zab a lardin Kirkouk ne wannan kashe-kashe suka afku.

Ita dai wannan ƙungiyar da ke da kaifin kishin addini ta yi ƙaurin suna wajen kashe-kashe a yanka jama'a kamar rago a yankunan da ke ƙarƙashin kulawarsu a Iraƙi da kuma Syriya. Kashe-kashen baya-bayannan dai sune na sojojin Syriya 18 da kuma wani dan amirka da take garkuwa da shi tun a shekara ta 2013. Tuni dai Majalisar Ɗinkin Duniya ta zargi ita IS da aikata laifin kisan kare dangi.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita. Abdourahmane Hassane