Ƙungiyar EU za ta tallafa wa Girka | Labarai | DW | 20.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙungiyar EU za ta tallafa wa Girka

Firaministan Girka Alexis Tsipras ya tattauna da shugabannin ƙasashen Jamus da Faransa da kuma hukumomin kuɗi na EU.

Ƙasashen dai na Ƙungiyar Tarrayar Turai sun yi alƙawarin tallafa wa ƙasar ta Girka da kuɗaɗen rance domin kiyayeta ga talauci tun da ga watan gobe.Amma bisa sharaɗin ƙaddamar da shirin tsuke bakin aljihun gwamnatin gabannin samun rancen na biliyan bakwai.

A share ɗaya kuma taron na Brussels ya sanar a cewar takunkumin karya tatalin arzikin da ƙasashen suka ƙaƙabawa Rasha.Zai ci gaba da kasancewa har sai yarjejeniya zaman lafiyar da aka cimma a gabashin Ukraine ta tabbata.