Ƙungiyar Boko Haram ta sake mamaye Marte | Labarai | DW | 16.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙungiyar Boko Haram ta sake mamaye Marte

Tuni da hukumonin jihar Borno da ke a yankin arewa maso gabashin Najeriya suka tabbatar da labarin.

Rahotanni daga Najeriya na cewar Dakarun Ƙungiyar Boko Baram sun sake karɓe iko da garin Marte da ke cikin jihar borno da ke a yanki arewa maso gabashin ƙasar.Wakilinmu na Gombe al Amin Suleiman ya shaida mana cewar tuni da hukumomin jihar suka tabbatar da labarin,sai dai dai kuma ya ce ba su ba da ƙarin haske ba dangane da cewar ko rudunar sojojin Najeriyar za ta mayar da martani da gaggawa

A cikin watannin da suka gabata ne rundunar sojojin Najeriya tare da tallafin wasu sojojin ƙasahe maƙwabta ta karɓe garin daga ckin hannu masu tadda ƙayar baya