Ƙungiyar Boko Haram ta kai hari a Kamaru | Labarai | DW | 20.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙungiyar Boko Haram ta kai hari a Kamaru

Majiyoyin tsaro na ƙasar sun ce an kashe jami'n tsaro ɗaya, yayin da ɗaya ya samu rauni a harin da aka kai a ƙauyen Nariki da ke kusa da Najeriya.

Jami'an tsaron suna yin sintiri ne a ƙauyen na Nariki da ke da ratan kilomita uku daga Amchidé a s'ailin da masu kishin addinin suka kai musu farmakin.

Ƙauyen na Nariki inda aka kai harin, yana kusa da garin Tarmoa da ke a cikin Najeriya inda Ƙungiyar ta Boko Hara ke da wata cibiya. A 'yan kwanakin baya-baya nan, ƙungiyar ta daɗa kai hare-hare a kan jami'an tsaro da sojoji na ƙasar ta Kamaru tare da aikata kisa da kuma sace jama'a. Kawo yanzu dai babu wata sanarwa da gwamnatin ta bayyana dangane da wannan batu.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman