Ƙungiyar ASUU ta janye yajin aiki | Labarai | DW | 17.12.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙungiyar ASUU ta janye yajin aiki

A Tarrayar Najeriya ƙungiyar malaman jami'a ta ASUU ta kawo ƙarshen yajin aikin da ta kwashe kusan watannin shida tana yi.

Jami'an ƙungiyar sun ce sun ɗage yajin aiki ne bayan yarjejeniyar da suka cimma tsakaninsu da gwamnatin, wacce ta zuba wasu tsabar kuɗaɗe domin tafiyar da harkokin jami'o'i a Najeriya.

A cikin watan Yuli da ya gabata ne ƙungiyar malaman jami'ar ta shiga yin yajin aikin,saboda zargin da ta yi wa gwamntin na gaza aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma a shekarun 2009.Wacce ta tanadi ƙara kuɗaɗen albashin na malaman da kuma samar da kayayyakin aiki ga jami'o'in Najeriyar.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe