Ƙungiyar Amnesty ta gano kamfanin Shell da yaudara a Najeriya | Labarai | DW | 03.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙungiyar Amnesty ta gano kamfanin Shell da yaudara a Najeriya

Tuni dai kamfanin na Shell me hakar albarkatun mai ya yi watsi da wannan rahoto na kungiyar Amnesty inda ya ce ya dukufa wajen ganin ya tsaffatace wuraren da ya bata.

Umweltverschmutzung im Nigerdelta

Yankin Niger Delta da ke fama da gurbatar muhalli

Ƙungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International ta ce ba kashin gaskiyya a shirin tsaffatace muhalli da kamfanin hakar albarkatun man fetir na Shell ke cewa yana yi a Najeriya.A rahoton da kungiyar ta fitar a ranar Talatan nan ta nunar da cewa daya daga cikin masu aikin kwantaragin tsaftar muhallin dubban al'ummar Najeriya da kamfanin ya lalatawa wuraren da suke cin abinci, ya ce aikin dai ana fadar cewa ana yin sa amma babu shi a kasa.

Tuni dai kamfanin na Shell ya yi watsi da wannan rahoto na Ƙungiyar Amnesty inda ya ce ya duƘufa wajen ganin ya tsaffatace wuraren da ya ɓata ciki kuwa har da yankin Ogoni inda sakamakon zanga-zangar da al'ummar yankin suka rika yi sai da kamfanin ya fice daga yankin a shekarar 1993.A cewar rahoton na Amnesty, kamfanin na Shell a Najeriya ba ya bin ƙa'idojin aikinsa yadda ya kamata kamar takwarorinsa a ƙasashen Turai.