Ƙungiyar ƙasashen larabawa na matsin lamba ga MDD a kan rikicin Lebanon | Labarai | DW | 09.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙungiyar ƙasashen larabawa na matsin lamba ga MDD a kan rikicin Lebanon

Tawagar ƙungiyar ƙasashen larabawa na cigaba da buƙatar kwamitin sulhu na Majalisar ɗinkin duniya ya gudanar da wasu gyare gyare a daftarin ƙudiri wanda zai kawo ƙarshen rikici tsakanin Israila da Hizbullah. Lebanon da sauran ƙasashen larabawa na yin matsin lamba ga majalisar ɗinkin duniya ta ƙara sanya buƙatar ficewar Israila daga ƙasar Lebanon baki ɗaya. Daftarin wanda Amurka da Faransa suka gabatar bai ambaci wannan buƙatar ba. Mai rikon mukamin Ministan harkokin wajen Lebanon Tareq Mitri yace Lebanon na buƙatar a gaggauta tsagaita wuta da kuma fadada sojin Majalisar ɗinkin duniya a kudancin kasar. A nasa ɓangaren jakadan Israila a Majalisar ɗinkin duniya Dan Gillerman ya buƙaci gamaiyar ƙasa da ƙasa su ɗauki managarcin mataki domin kwance ɗamarar Hizbullah da kuma dakatar da Syria da Iran daga baiwa kungiyar makamai.