Ƙungigoyin farar hula sun taka rawa a zaɓen Najeriya | Siyasa | DW | 02.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ƙungigoyin farar hula sun taka rawa a zaɓen Najeriya

Ƙungiyoyin fafutukar tabbatar da dimokraɗiyya na kan gaba cikin waɗanda suka taimaka aka tabbatar da zaɓe mai haske da adalci da kuma gaskiyya.

Wahl in Nigeria Wählerinnen in Jigawa

Masu kaɗa ƙuri'a a Jigawa

Ƙungiyoyin kare hakin jama'a da na tabbatar da dimokraɗiyya dai sun kasance hantsi leƙa gidan kowa bisa fafutukar da suka yi tun daga zamanin mulkin soja har zuwa sake kafa dimokraɗiyya a 1999. Irin yadda waɗannan ƙungoyi suka kasance ‘yan gaba-dai, gaba-dai wanda ya kai ga samun nasarar Janar Muhammadu Buhari ya sanya hasashen ƙalubalen da za su iya fuskanta wajen ci gaba da jajircewa Dr Abubakar Umar Kari masanin kimiyar siyasa ne da ke jami'ar Abuja.‘'Akwai waɗanda dama sun fasara wacce irin fafutuka suke yi, akwai waɗanda sun kafu ne a kan yadda za'a gyara zaɓe, waɗansu kuma 'yan neman kuɗi.''

Ƙungiyoyin wasu na yin aikin raya demokraɗiyya, wasu kuma kuɗi suke nema

Wahlen Nigeria Stimmabgabe Wahllokal Frau

To sai dai duk da gwagwarmayyar da suke yi ana yi wa wasu daga cikinsu kalon masu shiga rigar siyasa a Najeriyar, abin da ya sanya nuna damuwar ko za su iya ci gaba da jajircewa na ƙoƙarin tsawatawa duk wani shugaba, musamman zaɓaɓɓen shugaban Najeriyar Janar Muhammadu Buhari. Dr Hussani Abdu na cikin ƙungiyoyin da suke fafutukar tabbatar da dimokraɗiyya a Najeriyar.

‘'Ba wai tsunduma muka yi cikin harkokin siyasa ba ne don mu ba ‘yan siyasa ba ne, mun ga an fara yi wa dimokraɗiyya zagon ƙasa ne musmaman gwamnatin nan mai barin gado, don haka mun fara ɗaukan darasi daga wasu ƙasashe. Amma shi kansa Janar Buhari daga ranar da aka rantsar das hi daga nan kawai za mu fara sa kafar wando ɗaya da shi,za mu fara yi mashi matsin lamba.''

Ƙalubalen da ke a gaban ƙungiyoyin masu fafutuka na Najeriya

Wahlen in Nigeria

Tuni dai masu sharhi ke hangen ƙalubalen da ke gaban irin waɗannan ƙungiyoyi da dole ne su yi taka tsan-tsan domin kaucewa fuskantar hatsarin kaucewa layi kamar yadda Barrister Mainasara Umar mai sharhi a kan al'murran yau da kullum a Najeriya ya bayyana.‘'Allah ne ya baku amana ta al'ummar ƙasa da ke a kanku idan ba ku yi ƙoƙari ba kuna faɗin abubuwan da za ku gani gwamnati na yi ba dai dai ba, saboda kwaɗayi to kun ci amanar al'ummarku.''

A halin da ake ciki dai a yayin da ‘yan adawa ke ci gaba da shagalin nasarar da suka samu , za'a ci gaba da sa ido ga kamun ludayi da rawar da ƙungiyoyin da ke fafutuka za su taka don kaucewa shiga yanayi na zama ‘yan amshi shatar 'yan siyasa.

Sauti da bidiyo akan labarin