Ƙudirin tsige gwamnati a Nijar daga ′yan adawa | Siyasa | DW | 05.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ƙudirin tsige gwamnati a Nijar daga 'yan adawa

Jam'iyyun siyasa na Nijar sun gabatar da buƙatar ganin an kaɗa ƙuri'ar tsige gwamnatin saboda zargin yin sama da faɗi da dukiyar ƙasa.

Ɗaruruwan dokoki dai ne ke jiran majalisar dokokin Ƙasar ta Nijar da ta fara wani zamanta na musamman na tsawon watanni uku.Wanda kuma shi ne zaman ƙarshe da zai duba dokokin da gwamnati ta aike wa majalisar domin rataɓa hannu a kai. Ganin cewar nan da 'yan watanni ƙalilan ne za’a tinkari zaɓen 'yan majalisu da na mashawartan ƙananan hukumomin ƙasar ta Nijar.

Jam'iyyun siyasa na adawa sun ƙudiri aniyar kaɗa ƙuri'ar tsige gwamnatin

Seini Oumarou Kandidat Wahlen im Niger

Seyni Omar Ɗaya daga cikin shugabannin jam'iyyun siyasa na Adawa a Nijar, kuma shugaban MNSD

'Yan adawar ƙasar sun yi kira ga wakilansu da ke a majalisar dokokin da su karɓowa talakawa haƙƙoƙinsu ta hanyar kiraye-kirayen wasu ministoci manbobin gwamnati dangane da abin da 'yan adawar suka kira rashin iya jagoranci,
Honarable Sala Amadu Hassane ɗan majalisar dokokin na jam’iyyar adawa ne ta Lumana Afrika ya yi gargaɗin cewar za su yi abin da yakamata.'' Muna shirin aiwatar da umarni da kwamitin gabatarwa na Ƙungiyar 'yan adawar ya ba mu na ganin an kaɗa ƙuri'ar, mun san sun fi mu yawa amma duk da haka dai za mu buƙaci a kaɗa ƙuria'r,''

Babu dai shakku a zukatun ɓangaren gwamnatin cewar ƙuri'ar ba za ta yi nasara ba

Sitzung des Parlaments in Niger

Zaman taro a zauren majalisar dokokin Nijar

Da yake mayar da martani ɗan majalisar dokoki na jam'iyyar da ke mulkin PNDS Algabit Atta ya ce ba su da fargaba.'' Babu mazajen da za su zo su iya kaɗa ƙuri'ar, kuma idan suna da hujjoji, sai su jaraba amma mun san babu wata nasara da za su samu ko da an kai ga matsayin na kaɗa ƙuri'ar.''

Abin jira a gani dai shi ne yadda za ta kaya a majalisar a wannan sabon zama da ta dawo na watanni uku.

Sauti da bidiyo akan labarin