Ƙokarin magance matsalar tsaro a yankin Sahel. | Siyasa | DW | 06.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ƙokarin magance matsalar tsaro a yankin Sahel.

Tun bayan rikicin tawaye da aka sha fama da shi a ƙasashen Nijar, Mali, da Chadi, sannan ga rikicin ƙasar Libiya da ya haddasa bazuwar makammai, yankin Sahel da Sahara na fama da matsalar tsaro.

Wannan matsalar tsaron ta yankin Sahel da Sahara, ta ƙara bai wa duk wasu masu mummunar aniya damar samun wuraran zama a yankin, kamar masu safarar miyagun ƙwayoyi da duk wata safarar kayayyakin da ba'a aminta da su ba. Da yake magana kan wannan batu, Janar Maikido Garba, tsofon gwamnan jihar Agadez da ke arewacin ƙasar Nijar ya ce, "rikicin ƙasar Libiya ya sanya masu tada kayar baya sun kai ga rumbunan makamman ƙasar, inda suka yi awon gaba da dumbun makamman da a halin yanzu suka kasance babbar matsala ta tsaro a yankin na Sahel da Sahara, sannan ya ƙara da cewa barkewar rikicin kasar ta Libiya, ya kuma bai wa masu kaifin kishin addini damar shigowa yankin na Sahel inda sannu da hankali suka yi karfi a cikinsa tare da cin karansu ba babbaka har ma da neman kafa wani yanki na muslunci a kasar Mali."

Sai dai matsalar tashe-tashen hankullan da ake fuskanta a yankin na Sahel ba nan ka dai ta tsaya ba, domin kuwa ta shafi har da ƙasashen Turai. Bajan Ag Hamatou dan majalisar dokoki ne na ƙasar Mali wanda kuma yake a matsayin wani basarake na ƙabilar Abzinawa a yankin Menaka ya ce, "ƙasashen Turai su sani cewa amfani da ƙarfi kadai bazai yi maganin wannan matsala ba, sai an hada da kafa wasu cibiyoyin bunkasa rayuwar matasan yankin, ganin cewa da su ne ake amfani wajan tadda zaune tsaye ganin yadda talauci ya yi musu katutu, inda nan take suke amincewa da muyagun bukatun na 'yan ta'adda."

Shima tsofon ministan kiwon lafiyar ƙasar Nijar Issiyak Ag Kato, kira ya yi inda yake cewa, "ya kyautu a bai wa matasan na yankin Sahel da Sahara ilimi da tarbiya sannan da ba su horo a fannin koyon ayyukan hannu da duk wasu abubuwan da za su nesantar da su daga faɗawa ga mummunar ayyuka". Masana harkokin tsaro dai na ganin cewar, batun samar da zaman lafiya tare da sake gina ƙasar Libiya, shi ne zai iya dawo da kwanciyar hankali a yankin na Sahel.

Sauti da bidiyo akan labarin