Ƙoƙarin yin bincike a kan hatsarin jirgin sama na Ukraine | Labarai | DW | 19.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙoƙarin yin bincike a kan hatsarin jirgin sama na Ukraine

Masu aikin saka ido na Hukumar OSCE ta tsaro da ci-gaba ta nahiyar Turai na fuskantar cikas wajen gudanar da aikin bincike a inda jirgin saman Malesiya ya yi hatsari.

Har yazuwa yanzu sassan biyu sun gaza cimma matsaya guda wajen kilace zangon da ba za a iya kai hare-hare ba a wurin da hatsarin jirgin saman na Malesiya ya faru domin yin bincike. Tun da farko 'yan tawayen sun ba da izini ga jami'an hukumar waɗanda suka dakatar bayan sun fara aikin mintoci 30.

Kwamitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya buƙaci da a gudanar da bincike cikkake mai zurfi kana kuma mai zaman kansa. Wasu jami'an ofishin ministan agajin gaggawa na Ukraine wanda 'yan tawayen suka bai wa izini, sun ce sun gano gawarwakin mutane 186 a inda lamarin ya auku.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Suleiman Babayo