Ƙoƙarin yaƙi da talauci da kuma yunwa a duniya | Labarai | DW | 13.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙoƙarin yaƙi da talauci da kuma yunwa a duniya

Shugabannin ƙasashen duniya masu hanu da shuni da kuma na ƙasashe masu tasowa na taro a Addis Ababa domin samar da wata gidauniya don yaƙi da talauci da yunwa a duniya.

Wannan taro wanda irinsa shi ne na uku da ake yi bayan wanda aka yi a Monterey a Californiya a shekarun 2002 da kuma Doha a Qatar a shekarun 2008 a ƙarƙashin jagorancin Majalisar Ɗinkin Duniya.

Taron na da manufofin samar da wata gidauniya domin kyautata muradun ƙarni guda 17 na MDD na ci gaba mai ɗorewa.

An soma ƙaddamar da shirin daga wannan shekara ta 2015 zuwa 2030 na kawar da yuwan da kuma talauci a duniya kafin shekarun na 2030 da kuma daidaita lamura a kan canji yanayi.