Ƙoƙarin warware rikicin Siriya | Labarai | DW | 22.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙoƙarin warware rikicin Siriya

Shugaban ƙassar Siriya Bashar al Assad ya yi gargaɗin cewar babu alamun samun nasara a taron Jeniva wanda ƙasashen Rasha da Amirka suke son a yi.

A cikin wata hira da wani gidan telebijan n Libanon yayi da shi. Assad ya ce: ''A kwai buƙatar azza ayar tambaya kan cewar su wanene za su halarci taron, kuma wacce alaƙa suke da ita da a'ummar Siriya, suna wakiltar jama'a Siriya ne ,ko kuma suna wakiltar ƙasashen da suka ƙirƙiro su.''

Sannan kuma Assad ɗin ya ce bai ga wani abin da zai hana masa sake yin takara ba a zaɓen shugaban ƙasar na baɗi ba. Yau da aka shirya wasu ƙasashen yammancin duniyar guda 11 da wasu ƙasashen larabawa za su yi taro a Ingila a kan taron na Jeniva domin shawo kan 'yan adawar siriya su halarci taron.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane.
Edita : Saleh Umar Saleh