Ƙasashen yamma sun gaza warware rikicin Masar | Siyasa | DW | 30.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ƙasashen yamma sun gaza warware rikicin Masar

Su na ji suna gani ƙasashen yamma sun gaza sanya baki a rikicin Masar ta yadda zai yi tasiri mai a'ala ga al'umma, inda har yanzu rikicin ɓangarorin da ke taƙaddama ka ƙara ruruwa

Yau an wayi gari ƙasashen yamma sun sami kansu a tsaka mai wuya dangane da rikicin Masar. Ba za su iya fita fili su goyi bayan juyin juya halin da ya hamɓarar da Mohammad Mursi ba, kuma ba za su iya yin Allah wadai da shi ba, bugu da ƙari kuma, bacin waɗannan matakai, Amirka da ƙasashen Turai ba su da wani mataki mai ƙwari wanda zai matsawa Misrawan lamba su daidaita al'amuran ƙasar tasu.

Gwamnatocin ƙasashen yamma sun shiga wani mawuyacin hali a yanayin siyasarsu da Masar, shurun da suke ci gaba da yi bayan juyin mulkin da aka yi wa Mohammad Mursi ya sanya mutane tababan gaskiyar irin haƙiƙancewar da sukan yi kan buƙatar mutunta demokraɗiya da shikashikanta. Idan har suka yi Allah wadai da juyin mulkin da sojoji suka yi wa Mursi ranar 3 ga watan Yuli suka kuma ƙi yin aiki da gwamnatin wucin gadin da aka girka, to ko za su sami bakin magana a Alƙahira.

Ƙasashen yamma ba su da hurumin sanya baki

Bisa dukkan alamu, ƙasashen yamma suna so su ci gaba da iya riƙe ƙarfin faɗa a jin da suke da shi a ƙasar Masar a cewar Günter Meyer shugaban cibiyar da ke bincike kan Larabawa a Jami'ar Mainz da ke Jamus. Kuma wannan ya kasance haka ne saboda Masar na taka muhimmayar rawa a manufofinsu na Yankin Gabas Ta Tsakiya, domin na tsawon shekaru gommai yanzu, ita ce take shiga tsakani

"Da Amirka ce za ta iya matsa musu ƙaimi sosai kasancewar tana tallafawa ƙasar da kusan milliyan dubu ɗaya da rabi. Kuma akwai dokar da ta tanadi janya tallafin daga duk ƙasar da sojoji suka yi wa juyin mulki, shi ya sa Amirka ta ƙi yin amfani da kalmar juyin mulki wajen kwatanta abin da ya faru a Masar, amma abin da ya fito fili daga ɓarayin Amirka yanzu, shi ne wannan doka za a iya juya ta ta biya buƙatu da kuma son ran Amirka saboda haka ba za a iya amfani da ita a matsawa sojojin su janye juyin mulkin da suka yi ba ko ma ta kasance musu barazana.

Ko lokacin Mubarak an saɓawa shika shikan demokraɗiyya

Günter Meyer ya kuma ƙara da cewa, dakarun sojin na Masar sun sani sarai cewa Amirka bayansu take. Ba matakin matsin lamba ne kaɗai matsalar ba a wannan lamari har ma da rashin ɓangaren da ke mutunta demokraɗiyya amma kuma ba wannan ne karon farko da ƙasashen yammacin ke shiga tsaka mai wuya ba a cewar Christian Achrainer ƙwararre kan Masar a cibiyar da ke kula da harkokin zamantakewar ƙetare na Jamus, a shekarar 2011 lokacin da aka kifar da gwamnatin shugaban kama karyar ƙasar Hosni Mubarak, sun ce suna so a daidaita al'amura, amma kuma sai ya bayyana da cewa son ran Amirka da Turai ya karkata ga batutuwan da suka shafi samar da tsaro ta fuskar makamashi, yaƙi da ta'addanci da kuma ɗorewar yarjejeniyar sulhun da ke tsakanin Masar da Israila, duk wani batu na demokraɗiyya da kare haƙƙin ɗan adam, sai aka tura su baya

Ra'ayi na dangane da rikicin siyasar masar yanzu, shi ne idan har mutun yana taƙama da demokraɗiyya ne, to ko ba shi da ƙawa daga cikin ɓangarorin da ke saɓani da juna, akwai taƙaddama sosai tsakanin 'yan uwa musulmi da magoya bayan Mursi da kuma sojoji, kuma a ra'ayi na wanda ke hange da ƙasashen yamma, a cikin ɓangarorin biyu babu wanda ke goyon bayan demokraɗiyya, ke nan babu wanda za a iya marawa baya

Masu fashin baƙi dai na ganin cewa idan har an ci gaba da haka babu maslahar da za a samu saboda haka ya zama wajibi a ɗauki mataki na diplomasiyya.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Mohammad Nasiru Awal

Sauti da bidiyo akan labarin