Ƙasashen Yamma sun amince su bai wa Falasinawa taimako na wucin gadi. | Labarai | DW | 10.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙasashen Yamma sun amince su bai wa Falasinawa taimako na wucin gadi.

Rukunin bangarorin nan guda 4, da ke shiga tsakani don samad da zaman lafiya a Gabas Ta Tsakiya, ya amince da shirin kai taimakon agaji ga al’umman Falasɗinawa, waɗanda ke huskantar matsalolin rayuwa sakamakon dakatad da taimakon da aka yi daga ƙasashen Yamma, bayan lashe zaɓen da ƙungiyar Hamas ta yi. Sakatariyar harkokin wajen Amirka, Condoleeza Rice, ta ce shirin dai na wani ɗan gajeren lokaci ne. Kuma Ƙungiyar Hadin Kan Turai ce za ta zayyana tsarin shirin.

An ba da wannan sanarwar ne a Majalisar Ɗinkin Duniya a birnin New York, bayan da ministocin ƙasashen Larabawa suka yi gargaɗin cewa, ci gaba da tsai da ba da taimako ga Hukumar Falasɗinawa ƙarƙashin jagorancin Ƙungiyar Hamas, zai iya janyo wargajewar hukumar da kuma ɓarkewar yaƙin basasa.