Ƙasashen Turai sun yi tir da Isra′ila kan faɗaɗa matsugunai | Labarai | DW | 03.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙasashen Turai sun yi tir da Isra'ila kan faɗaɗa matsugunai

Birtaniya da Faransa da Sweden sun ba da sammaci ga jakadun Isra'ila don nuna adawa ga shirin Isra'ila na gina matsugunan Yahudawa a yankunan Falasɗinu.

Isra'ila na shan suka daga ko-ina a nahiyar Turai a dangane da shirinta na gina sabbin matsugunan Yahudawa a yankunan Falasɗinu. Gwamnatoci a biranen London, Paris da kuma Stockholm sun nemi ƙarin bayani daga jakadun Isra'ila a ƙasashensu a kan shirin ƙasar Yahudun Isra'ila na gina mastugunan da ake taƙaddama kansu. A wani abin da ba a saba gani ba shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta soki matakin Isra'ila da kakkausan lafazi. Kakakin gwamnati Steffen Seibert ya ce gwamnatin tarayya ta damu matuka da wannan shiri, wanda ya ce ya saka ayar tambaya ko da gaske Isra'ila ta ke na tattauna batun samar da zaman lafiya. Gina sabbin matsugunan dai zai zama wani babban batun a taron tuntubar juna tsakanin gwamnatoci da zai gudana a wannan Laraba a Berlin, inda ake sa rai firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu zai halarta. Bayan daga matsayin Falasdinu ta zama 'yar kallo a Majalisar Ɗinkin Duniya, Netanyahu ya ba da sanarwar gina sabbin mastugunan Yahudawa a gabacin Birnin Ƙudus da kuma Gabar yamma da kogin Jordan.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Halima Balaraba Abbas