Ƙasashen Georgia da Moldova na kusantar EU | Labarai | DW | 29.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙasashen Georgia da Moldova na kusantar EU

A yayin da wasu ƙasashen gabashin Turai ke ƙoƙarin kusantar Ƙungiyar Tarayyar Turai ta hanyar yarjejeniyar kasuwanci mara shinge, Ukraine ta ce a kai kasuwa

ITAR-TASS: VILNIUS, LITHUANIA. NOVEMBER 28, 2013. Ukrainian President Viktor Yanukovich meets for talks with President of the Council of Europe Herman van Rompuy and European Commission President Jose Manuel Barroso (from R) in Vilnius. (Photo ITAR-TASS / Mikhail Markiv) pixel

Janukowitsch na Ukraine da Barroso da Van Rompuy shugabanin Ƙungiyar Tarayyar Turai

Ƙasashen Georgia da Moldau waɗanda suka kasance a tsohuwar daular Sobiet sun fara yunƙurin komowa nahiyar Turai. Jagororin da ke wakiltar ƙasashen biyu da ƙungiyar Tarayyar Turai sun ɗauki matakin farko na rattaɓa hannu kan wata yarjejeniyar ƙawance, wadda ta tanadi ma'amala da kasuwanci mara shinge tsakaninsu, lokacin taron ƙolin Turan da ke gudana a ƙasar Lithuania

Ita kuwa Azerbaijan ta rattaɓa hannu ne kan yarjejeniyar da zai samar mata sassauci wajen samun takardun visa. Lokacin da yake jawabi a babban birnin ƙasar ta Lithuania wato Vilnius, Shugaban majalisar zartarwar Turai Jose Manuel Barroso ya siffanta waɗannan matakai a matsayin gagarumin cigaba, kuma ana sa ran a shekara mai zuwa, na 2014 ɓangarorin zasu rattaɓa hannu kan wannan yarjejeniya. Sakamakon matsin lambar da ta fiskanta daga Rasha, ƙasar Ukraine ta ƙi amincewa ta shiga wannan yarjejeniyar da Turai, sai dai shugaba Viktor Janokowich ya ƙarfafa cewa babu shakka nan gaba ƙasarsa za ta shiga irin wannan yarjejeniya.

Da take mayar da martani dangane da wannan batu, babbar kantomar da ke kula da harkokin wajen Turai Catherine Ashton ta yi tsokaci kamar haka

"Muna so mu sami dangantaka mai ƙwari da ƙasar Ukraine, mun yi imani sosai da batutuwan da suka shafi tattalin arziƙi, kuma akwai abubuwa da yawa da zamu iya yi tare dan cigaban mutanen Ukraine amma kuma ita ce kaɗai za ta iya yankewa kanta wannan shawarar"

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Umaru Aliyu