Ƙasashen duniya sun yi tir da kisan Alan Henning | Labarai | DW | 04.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙasashen duniya sun yi tir da kisan Alan Henning

Ƙungiyar masu jahadi wato IS ta yi iƙirarin kashe mutum na huɗu da take yin garkuwa da shi wani ɗan ƙasar Burtaniya.

Alan Henning ɗan shekarun kimani 47 da haifuwa wanda matuƙin Taxi ne da ya sa kansa aikin jinƙai na ba da tallafi wajen isar da kayan abinci a Siriya, Ƙungiyar ta sace shi a cikin watan Disamba na shekar bara.

Ƙungiyar ta IS ta bayyana bidiyon kisan na Alan a shafin Youtube da Twitter. Kuma ƙungiyar ta yi barazanar ƙara fille kan wani mutumin da take yin garkuwa da shi wani ɗan ƙasar Amirka wato Peter Kassig. Domin mayar da martanin ga hare-hare na taron dangin da ƙasashen yammancin duniya ke kai mata.