Ƙasashen duniya na fafutukar yaƙi da masu jihadi | Siyasa | DW | 25.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ƙasashen duniya na fafutukar yaƙi da masu jihadi

Kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya amince da sababbin matakai da za su taimaka wajen daƙile yaɗuwar ƙungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi irin su IS.

Baki ɗayan mambobin kwamitin 15 sun amince da sababbin matakan yayin wani taro na musamman da suka gudanar a jiya Laraba. A jawabin da ya yi shugaban Amirka Barack Obama wanda kuma shi ne ya jagoranci taron kwamitin sulhun, ya ce aƙalla masu kaifin kishin addini 15,000 daga ƙasashe 80 aka haƙiƙance sun tafi Siriya a 'yan shekarun nan domin yin abin da suke kira da sunan jihadi. Obama ya ƙara da cewar....

"Hana waɗannan mutane isa Siriya da kuma dawowa zuwa kan iyakokinmu wani babban ƙalubale ne a garemu wanda ya sanya tilas ne mu yi ƙoƙarin ruguza Ƙungiyar IS. Matakin na kan doka, samar da sababbin dokoki da dole sauran Ƙasashen duniya su bi".

Taron dangin na ƙasashen duniya a kan Ƙungiyar IS

Shi ma a jawabinsa, Sakatare janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki-moon cewa ya yi dole ne a ɗauki matakan gaggawa domin shawo kan matsalar tsaro inda ya ce tsawon lokaci matsalar masu kaifin kishin addini ce ta addabi zaman lafiyar duniya ba wai matsalar makamai masu linzami ba, don haka dole ne a magance ta'addanci.

: "Magance ta'addanci na buƙatar haɗin kan al'ummomin ƙasa da ƙasa. Daga cikin matakai masu yawa da ya zama wajibi mu ɗauka, dole ne mu yi ƙoƙarin magance matsalolin da suke haddasa samun ƙungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi.''

Nasarar samun haɗin kan ƙasashen duniya a kan yaƙi da ta'addanci

Sauran shugabannin ƙasashe kamar Francois Hollande na Faransa da kuma David Cameroon na Birtabiya da kuma Firaministan Tony Abott sun sha alwashin yaƙi da aiyyukan tarzoma da ta'addanci. Shugaba Hollande na Franasa ya ce tuni majalisar dokokin ƙasarsa ta ɗauki matakin hana mutanen da ake da zargi a kansu na cewar za su yi tafiyar ne domin zuwa wasu ƙasashen su gudanar da aiyyukan ta'addanci.

Sauti da bidiyo akan labarin