Ƙasashen Afirka na fafutukar yaƙi da Boko Haram | Labarai | DW | 31.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙasashen Afirka na fafutukar yaƙi da Boko Haram

Ƙasashe Maƙobtan Najeriya sun cimma yarjejeniyar murƙushe Ƙungiyar Boko Haram da sauran 'yan ta'adda a yankin.

Shugabannin ƙasashen yammacin Afirka sun yi alƙawarin haɗa hannu domin yaƙar 'yan ta'adda. Shugabannin sun sanar da haka yau Asabar a birnin Accra na ƙasar Ghana, a kwana na biyu na taron da shugaban Ghana John Dramani Mahama, wanda shi ne shugaban Ƙungiyar ECOWAS ya kira.

Taron ya tattauna hanyoyi da za a bi a yaƙi ƙungiyoyin 'yan bindiga da ke a arewacin Mali da Ƙungiyar Boko Haram a Najeriya. Shugabannin na ƙasashen na yankin yammancin Afirka da suka taru a birin Accra sun yi alƙawarin kafa wata hukumar haɗin gwiwa da za ta yi aiki a tsakiyar Afirka, domin ganin bayan 'yan ta'adda.Yanzu haka dai baya ga batun Boko Haram, akwai rikicin ƙabilanci da na addini a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, ga kuma rikicin abzinawa a arewacin Mali.

Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Abdourahamane Hassane