Ƙasar Spain ta fara mai da baƙin haure zuwa Senegal. | Labarai | DW | 14.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙasar Spain ta fara mai da baƙin haure zuwa Senegal.

Rahotanni daga birnin Madrid sun ce gwamnatin Spain, ta fara aiwatad da wani shiri na mai da baƙin hauren da suka zo neman mafaka a kan tsibirinta na Canaries zuwa Senegal. Ƙungiyoyin ba da taimamkon agaji da dama dai na adawa da wannan shirin. Amma duk da hakan, minstan kula da harkokin jin daɗin zaman jama’a na ƙasar, Jesus Caldera, ya ce za a yi jigilar farkon tawagar da ta ƙunshi baƙin haure dubu daga nahiyar Afirkan ne zuwa birnin Dakar na ƙasar Senegal. Sai dai bai ba da ƙarin bayani game da yadda za a awatad da shirin ba.

Amma ministan harkokin cikin gida na ƙasar Senegal ɗin, Ousmane Ngom, ya ce a shawarwarin da ya yi da mahukuntan ƙasar Spain, ƙasasrsa ta amince da karɓar baƙin, har da ma waɗanda ba su da wata takardar shaida. A cikin watan Mayun da ya gabata ne dai aka dakatad da shirin mai da baƙin, bayan koke-koken da ƙungiyoyin kare hakkin ɗan Adam suka yi ta yi game da abin da suke gani tamkar cin zarafin baƙin hauren. A cikin wannan shekarar kawai, kusan baƙin haure dubu 24 ne suka isa a kan tsibirin Canaries ɗin daga nahiyar Afirka, a cikin ƙananan kwale-kwale. Daya yawa daga cikin irin waɗannan kwale-kwalen kuma sun nitse da mutanen da suke ɗauke da su kafin isa a tsibirin.

A halin da ake ciki yanzu dai, wani rukunin jami’an tsaron iyaka na ƙungiyar Haɗin Kan Turai ya fara sintiri cikin jiragen ruwa a kan teku kusa da ƙasashen Afirka Ta Yamma, don hana baƙin hauren yin ƙaura zuwa nahiyar Turai.