Ƙasar Italiya ta ceto bakin haure | Labarai | DW | 31.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙasar Italiya ta ceto bakin haure

Sojojin ruwan na Italiya sun ceto baƙin haure masu neman shiga Turai sama da dubu uku.

Sojojin ruwan Italiya da ke bakin gaɓar ruwan ƙasar sun bayyana ceto baƙin haure fiye da 3,500 da suka haɗa da ɗaruruwan mata da yara, waɗanda suka fito daga arewacin Afirka. Hukumomin ƙasar suka tabbatar da haka, a lokacin da Firamnistan ƙasar Matteo Renzi ya yi kira kan neman taimako daga Ƙungiyar Tarayyar Turai.

An ceto baƙin haure 'yan arewacin Afirka da Siriya sakamakon aikin da aka gudanar tun daga daren Jumma'a, kuma mafi yawan baƙin haure sun fito ne daga Siriya. Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce rashin gwamnatoci na gari a ƙasashen arewacin Afirka tun bayan juyin-juya hali ya ƙara dagula lamura. Yanzu haka baƙin hauren da aka ceto suna a tashoshin jiragen ruwa na Sicily da Lampedusa da ke ƙasar ta Italiya.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Abdourahamane Hassane