Ƙaruwar ayyukan Alƙa′ida a Yamen | Labarai | DW | 24.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙaruwar ayyukan Alƙa'ida a Yamen

Ƙungiyar Alƙa'ida na ƙara gigita al'amura a ƙasar Yamen, inda gwamnati ke fafatawa da mayaƙan ƙungiyar.

Forensic policemen collect evidence at the site of a suicide bomb attack at a parade square in Sanaa May 21, 2012. A uniformed man blew himself up in the midst of a military parade rehearsal attended by senior officials in the Yemeni capital Sanaa on Monday, killing at least 41 people and wounding more than 60, a police source said. REUTERS/Khaled Abdullah (YEMEN - Tags: POLITICS CIVIL UNREST CRIME LAW)

Wani harin ta'addanci da aka kai a Yamen

A yammacin wannan Talata ne dai ƙungiyar ta Alƙa'ida, ta sako wasu 'yan sanda 21 da ta kame, a wani mummunan farmakin da ta kai makon jiya. Wata majiya ta ce a yankin da ƙabilu suke iko da shi kan tsaunuka aka sako 'yan sandan, waɗanda aka kama a wani sansaninsu da ke yankin. An dai kama 'yan sandan ne bayan wani kwatan ɓauna da aka yi musu a ranar Juma'an da ta gabata. Ƙungiyar Aka'ida dai na da matukar ƙarfi a ƙasar Yamen, musamman a yankunan gabashi da kudanci, inda babu wata hukuma mai ƙarfi da iko a wajen. Ƙasar Yamen a yanzu haka ita ce inda ƙungiyar Alƙa'ida ke horar da mayaƙa, waɗanda ke aikata munanan ayyuka a yakin ƙasashen Larabawa da ma wasu ƙasashen Afirka.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Saleh Umar Saleh