Ƙarin bayani kan masu yaƙi da muggan laifuka | Masu Yaki da Muggan Laifuka | DW | 26.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Yaki da Muggan Laifuka

Ƙarin bayani kan masu yaƙi da muggan laifuka

Labaran masu gudanar da binciken sirri a sabon wasan kwaikwayon DW na kokarin warware matsalolin da matasa ke fuskanta ne a Afirka.

Ku biyo masu binciken wajen gwagwarmayar neman gaskiya da adalci a kan batutuwa masu mahimmancin gaske, waɗanda suka haɗa da shiga ta'addanci, da satar dabbobi, da ƙwace filaye da kuma amfani da magungunan jabu. A yayin da take ci gaba da ƙidayar nasarorin da ta samu a shirinta na Ji Ka Ƙaru mai ilimantarwa, salsalar shirin Masu Yaƙi da Muggan Laifuka zai fayyace wa masu sauraro muhimman batutuwa cikin nishaɗi, ta yadda za su yanke shawarar da ta fi dacewa a duk lokacin da suka gamu da irin waɗannan matsalolin.

Fitaccen marubucin adabi a fannin muggan laifuka Mukoma Wa Ngugi (Kenya) ya rubuta labarin magungunan jabu, a yayin da Helon Habila (Najeriya) da Andrew Brown (Afirka ta Kudu) suka tallafa wa shirin a matsayin masu bayar da shawarwari.

'Yan wasa daga duk faɗin nahiyar Afirka suka taka rawa wajen ganin wannan wasa ya zo gare ku. Kowanne daga cikin labaran huɗu na da tsawon minti 10, kuma za ku iya sauraransu a harsunan Ingilishi, Kiswahili, Faransanci, Hausa da kuma harshen Portugal. Tashar DW tana watsa wannan shiri tare da abokan hulɗartar 250 sannan kuma ana mahawarori kansu a kafofin sada zumunta.

Yaƙi da Muggan Laifuka: 'Yan Ra'ayin Riƙau

Bam ya tashi a wani rukunin kantuna a ƙasar Kadaura kuma wasu 'yan sanda matasa Jibrin da Binta na kan wannan binciken. Nan da nan kuwa, suka gano cewa harin kunar baƙin wake ne, kuma wata mace ta aikata. Abin ban mamaki ma shi ne asalinta a rayuwa. Sunanta Zahra Kassim - ta kammala jami'a ke nan da daraja ta farko, kuma mahaifinta sanannen ɗan siyasa ne. Me ya sanya ta yin wannan aika-aikar? An tilasta mata ne? Ko kuwa da son ranta ta yi? Jami'an 'yan sandan sun yi amfani da dabaru da dama har ma sun sanya kansu cikin haɗari. Jibrin da Binta sun yi aiki sosai wajen gano duk dalilan da ke jan hankalin matasa zuwa ta'addanci, sai dai daga ƙarshe, manufar Zahra ta kasance wani abun na daban wanda bai yi kama da abin da suka zata tun farko ba.

Yaƙi da Muggan Laifuka: 'Yan Farauta Daɗi

Jami'an 'yan sanda biyu, bincike biyu. Ɗan sanda Aliyu na binciken kisan wani likitan dabbobi mai suna Ilyasu. Abokin aikinsa Sanusi na neman wani wanda aka fi sani da Malam Aboki, shugaban wani gungun masu satar dabbobi da ke ci gaba da janyo matsala a garin Bovu. Suke kashe giwaye da mugun dawa da damisa, kuma yawancin irin waɗannan dabbobi na dab da gushewa. Muhalli da ma tattalin arziki na ci gaba da fuskantar koma baya a dalilin ayyukan waɗannan mutane, waɗanda suke kwasar miliyoyin kuɗi ta haramtacciyar hanya. Sai dai masu binciken sun gano bakin zaren ne lokacin da aka gano wata wasiƙa a kayan marigayi Iliyasu, wanda ke barazanar bata masa suna, da kuma fallasa asalin mutumin da ake kira Malam Aboki. Shin wanda ya kashe Iliyasu ya san ko wane ne Malam Aboki? Dalilin da ya janyo ajalinsa ke nan? Daga ƙarshe dai gaskiyar ta ma fi ba da mamaki.

Yaƙi da Muggan Laifuka: Garin Danya

Gawar Maigari Ibrahim na kwance a bakin kogin da ke kusa da gonar furanni. Namun daji ne suka hallaka shi kamar yadda gwamnatin Danya take so su amince? Ko kuwa dai kashe shi aka yi? Wasu na zargin haka domin gonar furannin ta kasance mallakar Maigari Ibrahim. Gwagwarmaya ya yi sosai don tabbatar da cewa al'ummarsa ce ta ci moriyar wannan fili a maimakon miƙa ta ga masu zuba jari daga ƙasashen ketare. Sifeto Lawan na tsaka mai wuya, ya rasa ko ya amince da labarin da mahukunta suka bayar ko kuma ya bi zuciyarsa ya binciki ainihin abin da ya faru. Ramatu ce ta fara binciken gano gaskiyar. Ta gano cewa batun filin na tattare da sarƙaƙiya fiye da yadda suka zata tun farko, hasali ma tun kafin a kai ga samun 'yancin kai kuma takardun filin ba daidai suke ba. Turka-turkar ba ta tattalin arziki kaɗai ce ba har ma da batutuwa masu sosa rai. Anya Ramatu za ta iya gano wanda ya kashe Maigari Ibrahim kuwa?

Yaƙi da Muggan Laifuka: Ga Maganin Waraka ga na Kisa

Salim ɗan wani hamshaƙin mai kuɗi ya rasu bayan da ya sha wasu ƙwayoyi ba bisa ƙa'ida ba. Sai dai da aka yi wa gawarsa binciken kokof sai aka gano cewa ba kashe kansa ya yi ba, guba ce aka sanya masa. A dalilin haka ne masu bincike Kamilu, Mansur da Salama, suka ƙaddamar da bincike inda suka ci karo da abubuwa masu ban mamaki, da haɗama da kuma tashin hankali. Domin gano wanda ya kashe Salim, sai da suka shiga kasuwar masu sayar da jabun magunguna waɗanda ke amfani da marasa lafiya wajen cimma burinsu. Magungunan jabu suna da araha sosai, kuma mutane da yawa ba su san haɗarin da yake da shi ga lafiya ba. Wasu bayanai sun kai su ga wani ƙwararren likita, da wani mai maganin gargajiya, da ƙwararre kan haɗa magunguna har ma da ministan lafiya. Masu binciken sun sanya rayukansu a haɗari sosai. Sai dai daga ƙarshe sun gano rawar da Salim ya taka da ma dalilan da suka kai ga mutuwarsa.