ƙalubalen harkokin tsaro a ƙasar Masar | Labarai | DW | 19.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

ƙalubalen harkokin tsaro a ƙasar Masar

Shugaban gwamnatin wucin gadi Adli Mansur ya yi gargaɗin cewar za su dawo da doka da kuma kwanciyar hankali a Masar.

(Soldaten vor Stacheldraht mit gepanzerten Manschaftstransportern auf der Islamistendemonstration in Kairo; 9.7.13) Bildunterschrift: Soldaten der Armee versperren den Zugangsweg zu einem Stützpunkt der Republikanischen Garde / DW/M. Sailer

Ägypten Unruhen Militär 9. Juli 2013

Shugaban ya bayyana haka ne a cikin wani jawabi da ya yi a jiya alhamis ta gidan talabijan na ƙasar, wanda a ciki ya zargi wasu mutane da neman saka kasar cikin tashin hankali ta bin hanyar zubar da jini. Sannan kuma ya ƙara da cewar ''muna cikin wani mayuwacin hali wanda wasu suke son sun yi amfani da wannan damar don kawo mana ruɗani. Amma za mu yi maganin lamarin.''

Wannan jawabi na sa na zuwa ne a daidai lokacin da magoya bayan tsohon shugaban ƙasar Muhammed Mursi suka shirya yin zanga-zanga a yau bayan sallah Jumma'a, domin matsa ƙaimi ga hukumomin da su sake mayar da Mursi a kan mulki, wanda sojoji suka yi masa juyin mulki a farkon wannan wata.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe